Edo ta taba aure da hamshakin dan kasuwa Philip Ehiagwina a shekarar 2008 amma sun rabu a shekarar 2014.
Washington D.C. —Jarumar Nollywood a Najeriya, Ini Edo, ta sanar da cewa ta yi za ta amarce da angonta.
Ini Edo ta bayyana hakan a wani sako ta shafinta na Instagram, @iniedo, a ranar Lahadi.
"Wannan safiyar Lahadi mai haske watanni shida da suka wuce, yayin da nake hutu, mun hadu da juna, kuma rayuwarmu ba ta sake zama iri daya ba.” Edo ta ce.
“Daidai watanni uku bayan haka ka tambaye ni in kasance tare da kai har abada. Ta yaya na yi sa’ar haka?”
Edo ta taba aure da hamshakin dan kasuwa Philip Ehiagwina a shekarar 2008 amma sun rabu a 2014.