Onwenu ta rasu ne a ranar 30 ga Yulin shekarar 2024, a asibitin Reddington da ke Ikeja a jihar Legas.
Washington D.C. —Rhotanni daga Najeriya na cewa a ranar Juma’ar nan ake jana'izar shahararriyar mawakiyar Najeriya, Onyeka Onwenu, a jihar Legas.
Onwenu ta rasu ne a ranar 30 ga Yulin shekarar 2024, a asibitin Reddington da ke Ikeja, bayan faduwarta a wani taron karrama Dr. Stella Okoli, Manajan Darakta ta Emzor Pharmaceuticals.
A cewar wani shiri na jana’izar da ‘yan uwata suka yi, za a yi taro na tunatarwar ne a cocin Fountain of Life Church Ilupeju.
Sannan kuma za a yi jana’izar ta ta a sirrance a wani wajen adana na musamman da ke Ikoyi, kamar yadda labaran CKN News ya ruwaito.
An haife Onyeka Onwenu ne ranar 31 ga Janairu 1952. Ita ce karamar diyar masanin ilmin Najeriya kuma dan siyasa D. K. Onwenu, wanda ya rasu tana da shekaru hudu da haihuwa, mako guda kafin a nada shi a matsayin Ministan Ilimi.