Hukumar Shige Da Fice Ta Kama Bobrisky A Iyakar Najeriya Da Benin

Hukumar Shige Da Fice Ta Kama Bobrisky A Iyakar Najeriya Da Benin

Hukumar ta ce Bobrisky na kokarin tserewa hukuma ne a lokacin da aka cafke shi.

Washington D.C. — 

Hukumar shige da fice ta Najeriya ta ce ta kama Okuneye Idris Olanrewaju da aka fi sani da Bobrisky a iyakar Seme da ta hada Najeriya da Jamhuriyar Benin.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin X a daren Litinin, hukumar ta ce ta kama Bobrisky ne yayin da yake “kokarin tserewa daga kasar.”

“Hukumar tana so ta sanar da jama’a cewa, Okuneye Idris, mutum ne da ake nema kan wani al’amari da ya shafi jama’a.

“Ana kan yi masa tambayoyi kuma za a mika shiga ga hukumar da ta dace.” Sanarwar dauke da sa hannun Kakakin hukumar, DCI Kenneth Udo ta ce.

Kwamitin Majalisar Wakilai da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), da Hukumar Gidajen Yari ta Najeriya na binciken Bobrisky kan zarge-zargen da suka shafi ba da cin hanci.

‘VeryDarkMan’ da ya yi fice a shafukan sada zumunta ne ya fitar da wani faifan sauti da aka ji Bobrisky yana ikirarin cewa ya biya wasu jami'an EFCC naira miliyan 15 domin su janye zarge-zargen halalta kudaden haram da ake masa.

Bobrisky ya sha musanta cewa muryar da aka ji a cikin faifan sautin ta shi ce.


News Source:   VOA (voahausa.com)