Hotunan abubuwan da suka faru a Kannywood a wannan makon23 Feb 2020, 19:30Hakkin mallakar hotoIntagram/realabmaishaddaImage caption Furodusa Abubakar Bashir Maishadda ya samu karuwa ta haihuwa. Matarsa ta haifi zankadediyar budurwa wadda ya wallafa hotonta a shafinsa a ranar Asabar. 'Yan uwa da masoya da abokan sana'a na ta addu'o'in taya murna Hakkin mallakar hoto@realalinuhuImage caption Editan Kannywood Yakubu Usman Mpeg, ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa a ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu. Jaruman masana'anta da masoyansa sun yi ta aika masa sakonnin taya murna Hakkin mallakar hoto@officialkannywoodImage caption Dambarwa ta kunno kai bayan Yusuf Haruna (Baban Chinedu) ya zargi shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Isma'il Na'Abba Afakallahu, da karkatar da naira miliyan biyar da gwamantin jihar Kano ta bayar a matsayin gudummuwa a lokacin bikin diyar marigayi Rabilu Musa Ibro Hakkin mallakar hoto@nura_m_inuwaImage caption Ko dai an yi wa Nura M Inuwa nadin sarauta ne? A wace masarauta, kuma wace saurauta aka ba sh? Irin wannan nadi haka! Hakkin mallakar hoto@officialkannywoodImage caption Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ce dole tauraron Kannywood Adam Zango ya bi dokokinta idan yana so ya je jihar domin gudanar da harkokin fim. Hakan na zuwa ne bayan bidiyon da Rahama Sadau ta wallafa na Zango yana cewa zai je Kano domin kallon fim din 'Mati A Zazzau'. Hakkin mallakar hoto@namenjImage caption Namenj ya fitar fitar da hotonsa a lokacin daukar wata waka da ya yi cikin harshen turanci. Hakkin mallakar hoto@mustapha_nabraskaImage caption Allah Ya raya 'yan mata, Ya kara wa mai jego lafiya! Jarumi Mustapha Nabraska ya samu karuwar 'ya mace a ranar Asabar 22 Fabrairu, 2020. Image caption Tauraruwar Kannywood, Aisha Dankano ta cika shekaru hudu da rasuwa. Allah Ya garfarta mata, mu ma idan ta mu ta zo Allah Ya sa mu yi kyakkyawan karshe