Fitacciyar mawakiyar nan ‘yar Najeriya Onyeka Onwenu ta rasu a asibitin Reddington da ke Legas bayan da ta yanke jiki ta fadi a wajen wani bukin murnar zagayowar shekarar haihuwa.
Washington, DC —Rahotanni na nuni da cewa, marigayiyar ta gama waka a wajen bukin zagayowar ranar haihuwar Misis Stella Okoli, ta je ta zauna ke nan sai ta yanke jiki ta fadi daga nan aka garzaya da ita asibiti inda aka tabbatar rai ya yi halinsa.
An haife Onyeka Onwenu ne ranar 31 ga Janairu 1952. Ita ce karamar diyar masanin ilmin Najeriya kuma dan siyasa D. K. Onwenu, wanda ya rasu tana da shekaru hudu da haihuwa, mako guda kafin a nada shi a matsayin Ministan Ilimi.
courtesy XOnyeka Onwenu ta yi makaranta a ciki da wajen Najeriya. Ta yi karatu a fanin hulda da jama’a da sadarwa a wata Jami’ar Amurka dake jihar Massachusetts, da kuma yi karatu a fannin nazarin zamantakewa a wata jami’ar dake birnin New York.
Marigayiyar tayi aiki a tashar talabijin ta kasa NTA inda ta gabatar da shirye shirye da suka yi fice da dama. Ta kuma zama member kwamitin darektocin tashar ta NTA.
Onyeka Onwenu ta fara wake-wake a shekarar 1981 lokacin tana aiki da NTA. daga baya ta koma yin wakokin bishara a cikin shekara ta 1990, Ta ci gaba da yin rubuce-rubuce da wakaki kan batutuwan da suka shafi kiwon lafiya (HIV/AIDS), zaman lafiya, da zaman tare, mutunta ’yancin mata, da halin da yara ke ciki. Tana kuma wallafa shawarwari ga mata a dandalin sada zumunta na X.
Marigayiyar ta kuma yi fice a fannin wasannin fina-finai da ake nunawa a gidajen talabijin a wancan lokacin.
Onwenu ta kuma shiga siyasa ta tsaya takara karkashin tutar jam'iyyar PDP. Ta yi takarar zama shugabar karamar hukumarta Ideato ta Arewa a jihar Imo har sau biyu amma bata sami nasara ba. Daga baya, tsohon gwamnan jihar Imo Ikedi Ohakim ya nada ta Shugabar Majalisar Fasaha da Al’adu ta Jihar Imo. A ranar 16 ga Satumba, 2013, Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya nada ta Babbar Darakta, kuma Babban Jami’ar Cibiyar Bunkasa Rayuwar Mata ta Kasa.
A shekara ta 2000, Onwenu ta yi zanga-zangar adawa da tsohuwar ma’aikatarta ta NTA saboda kin biyanta kudaden amfani da wakokinta, bayanda tashar NTA 5 ta yi amfani da "Iyogogo",daya daga cikin wakokinta ba tare da neman izininta ba. Ta kuma fara yajin cin abinci bayan da darekta Janar na NTA a lokacin Ben Murray-Bruce ya hana ta fitowa a a tashar baki daya.
onyeka OnwenuYunkurin Onwenu ya jawo goyon baya daga masu fasaha daban-daban, ciki har da Charly Boy, wanda ya yi Allah wadai da yadda Najeriya ke kin biyan kudaden tukuici a lokacin da ake yada wakoki a talabijin da rediyo. NTA ta yanke shawarar sasanta lamarin cikin ruwan sanyi amma ta musanta hana Onwenu fitowa a tashoshinta. Onyeka Onwenu ta dakatar da zanga-zangar bayan kwanaki shida lokacin da Onwenu da NTA suka tsaida yarjejiniya kan tukuicin mawaki.
Onyeka Onwenu ta rasu tana da shekaru 73 a duniya, ta bar ‘ya’ya maza biyu.
Tuni aka shiga rubuta sakonnin jimamin rasuwar mawakiyar a kafafen sada zumunta
Embed A Yada DARDUMAR VOA: Allah Ya Yi Wa Jaruma Daso Saratu Gidado Rasuwa Embed A Yada The code has been copied to your clipboard. width px height px Nuna wa mutane akan Facebook Nuna wa mutane akan Twitter The URL has been copied to your clipboard Auto240p360p480p720p1080pNo media source currently available
0:00 1:20 0:00 Auto240p360p480p720p1080pGrace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.
Subscribe