Fitaccen Furodusa Quincy Jones Ya Rasu

Fitaccen Furodusa Quincy Jones Ya Rasu

Jones ya kuma ya yi alaka da shugabannin kasashe da manyan mutane, taurarin fina-finai da mawaka da manyan ‘yan kasuwa.

Washington D.C. — 

Shahararren furodusa waka a Amurka Quincy Jones ya rasu yana da shekaru 91. Wani Mai kula da al'amuransa ya ce ya rasu ne daren Lahadi a gidansa da ke Los Angeles a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na AP.

Jones ya kasance furodusan da ya samar da kundin wakoki na Michael Jackson mai suna “Thriller” wanda ya kafa tarihi.

Ya kuma samu lambar yabo a fannin kida da fina-finai, tare da hadin gwiwa da Frank Sinatra da Ray Charles.

Quincy Jones (Dama) Michael Jackson (Hagu)a bikin ba da lambar yabo ta Grammy Award a shekarar 1984 Quincy Jones (Dama) Michael Jackson (Hagu)a bikin ba da lambar yabo ta Grammy Award a shekarar 1984

Jones ya fice daga makarantar koyon kade-kade ba tare da ya kammala ba amma daga baya ya shahara har ya zama mashahuri inda ya zama daya daga cikin bakaken fata na farko da suka yi fice a masana’antar Hollywood.

Cikin shekaru 60 da suka gabata, ya kasance da wuya a samu wani a cikin masana'antar waka ko talabijin ko fina-finai wanda bai yi wata alaka da Jones ba.

Jones ya kuma ya yi alaka da shugabannin kasashe da manyan mutane, taurarin fina-finai da mawaka da manyan ‘yan kasuwa.


News Source:   VOA (voahausa.com)