Hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano ta ce dole tauraron fina-finan Kannywood Adam A. Zango ya bi dokokinta idan yana so ya je jihar domin gudanar da harkokin fim.
A ranar Juma'a ne Adam A. Zango ya fito a wani bidiyo da Rahama Sadau ta wallafa a Instagram yana yi wa masoyansa Kanawa albishirin cewa zai je jihar domin kallon fim din 'Mati A Zazzau'.
Sai dai jim kadan bayan hakan ne wasu kafafen sadarwa na zamani suka ambato shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar, Isma'ila Na'abba Afakallah, yana shan alwashin kama tauraron idan ya sanya kafarsa a jihar.
Amma a tattaunawarsa da BBC, Afakallah ya ce ba su hana tauraron shiga jihar ba amma suna da dokoki game da zuwansa.
"Idan zuwa zai yi ya kalli fim kawai ya tafi shikenan, akwai wadanda ba su da rajista kuma suke zuwa su yi kallon su tafi babu ruwanmu da su.
"Kwanakin baya wannan hukumar ta yi kokarin tantancewa da tsafetace masu ruwa da tsaki a wannan harka kamar yadda doka ta ba ta dama."
'Ba shi da rajista a Kano'
"An samu mafi yawa daga cikinsu sun zo sun yi amma shi (Adam Zango) yana cikin wadanda ba su yarda su yi hakan ba, har ma ya ce ya fita daga tsare-tsarenmu."
Da aka tambaye shi ko ba ya ganin hakan tauye hakkin Zango ne na yin taro ba tare da tsangwama ba kamar yadda tsarin mulki ya ba shi dama?
Afakallah ya amsa da cewa: "Don an ba ka 'yanci ai kuma akwai inda 'yancin wasu za ka taka."
Rayuwar Adam A Zano a takaice
- An haife shi a garin Zangon Kataf a jihar Kaduna
- Ya bar garin a 1992 bayan rikicin kabilancin da aka yi
- Ya koma arayuwa a jihar Plateau inda ya yi karatun Firamare
- Talauci ya hana shi cigaba da karatu a wancan lokacin
- Tun yana yaro ake masa lakabi da Usher - mawakin nan dan Amurka saboda yadda yake rawa
- Ya koma Kano inda ya fara aiki a wani kamfanin kade-kade da raye-raye
- Fim dinsa na farko shi ne Sirfani, wanda ya ce shi ya shirya shi da kansa
- Ya fito a fim sama da 100 a tsawon shekara 16
'Zan ba da kyautuka'
BBC ta yi yunkurin jin ta bakin Adam Zango, sai dai wayarsa a kashe take kuma bai amsa sakon da muka aika masa na text ba.
Sai dai tun da farko tauraron ya sha alwashin gwangwaje magoya bayansa idan ya samu damar zuwa Kano.
"Kanawa ku shirya, zan kasance tare da ku domin kallon fim din Mati A Zazzau a ranar Lahadi da kuma Litinin," Zango ya fada tare da Rahama Sadau a gefensa.
"Sannan kuma akwai kyauta ta musamman da zan bai wa masoyana, mace da namiji."
- Me ya sa gwamnatin Ganduje ke takun-saka da mawakan Kannywood?
- Cikin hotuna: Abubuwan da suka faru a Kannywood makon jiya
'Na fita daga Kannywood'
A watan Agustan 2019 ne Adam A. Zango ya ce ya fita daga kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Kannywood.
Tauraron fim din kuma mawaki ya ce daga yanzu zai fara cin gashin kansa ne, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Instagram.
Sai dai bai yi karin haske ba game da abin da yake nufi da fita daga kungiyar, ganin cewa akwai kungiyoyi da dama da suke cikin Kannywood.
Amma ya yi zargin cewa "ana yin shugabancin kama karya da rashin hukunta mai karfi ko arziki saboda kwadayi da son zuciya.
'Tuni na fara harkokina a Legas'
Kazalika, a watan Disamba dan wasan ya shaida wa jaridar Aminiya cewa shi fa ya koma jihar Legas da harkokinsa.
"Kamar dalibin ilimi ne da ya kammala karatun sakandare, idan yana so ya ci gaba da karatu sai ya tafi makarantar gaba da sakandare ko ya je jami'a, wannan ita ce manufata.
"Tuni na fara harkokina (a Legas), komai ya kankama. Ina shirin cikin wata shida zuwa shekara ɗaya zan dawo da iyalina gaba ɗaya nan Legas, har da mahaifiyata, cikin yardar Allah."
Karin labarai da za ku so karantawa: