Da A Ce Akwai Ingantacciyar Manhajar Fina-finan Hausa, Da Yanzu Mun Yi Kudi – Tijjani Asase

Da A Ce Akwai Ingantacciyar Manhajar Fina-finan Hausa, Da Yanzu Mun Yi Kudi – Tijjani Asase

Asase ya bayyan hakan ne yayin wata hira da ya yi da shirin “Darduma” na Sashen Hausa na Muryar Amurka.

Washington D.C. — 

Fitaccen jarumin masana’antar Kannywood da ke arewacin Najeria Tijjani Asase, ya ce samar da wata manhaja ingantacciya da za ta rika ba da dama ana kallon fina-finan Hausa zai taimakawa masana’antar wajen samun kudaden shiga masu kauri.

Asase wanda ya fito a manyan fina-finai irinsu ‘Gidan Badama’ da ‘A Duniya’ ya ce harshen Hausa na daga cikin manyan harsuna na gaba-gaba da zai iya shiga sahun manyan harsuna biyar ko goma na duniya.

“In aka ce za a yi wannan manhaja a ce za a samu fim din Hausa, sai an tantance, ya kai matsayin da yanzu da ni da ke da ‘yan boka da dan gargajiya zai shiga wannan manhaja ya kalli fim da zai burge, shi ai da yanzu duk mun zama masu kudi.” In ji Asase.

Asase ya bayyan hakan ne yayin wata hira da ya yi da shirin “Dardumar VOA” na Sashen Hausa na Muryar Amurka.

Jarumin wanda har ila yau yana shirya fina-finai ya kara da cewa harkar fim a yanzu ta banbanta da yadda take a baya.

“A bangaren mata, matanmu na da sun iya kashe kudi amma ba su san neman kudi ba, na yanzu kuma sun san darajar neman kudi, babu wata yarinya da za ta yi suna ba ka ji tana wata ‘yar sana’a ta saye da sayar wa ba.” Asase ya ce.

Ya kara da cewa, a da, akwai wasu dabi’u da ake iya nunawa a fina-finan Hausa wadanda ba a saka su a yanzu yana mai buga misali da yadda mu’amulla take tsakanin namiji da mace.


News Source:   VOA (voahausa.com)