Cikin hotuna: Abubuwan da suka faru a Kannywood makon jiya16 Feb 2020, 04:10Hakkin mallakar hotoInstagram/realsanidanjaImage caption Ranar Litinin tauraro Sani Danja (dama) ya wallafa hoton ziyarar da suka kai wa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed (tsakiya) tare da amininsa, Yakubu Mohammed (hagu) domin taya shi murnar yin nasara a kotun koli. Hakkin mallakar hotoInstagram/khadejah_mustaphaImage caption Ranar Laraba Khadija Mustapha ta yi murnar zagayowar ranar haihuwarta, wato birthday Hakkin mallakar hotoInstagram/InstagramImage caption ...A ranar ne tauraruwa Rahama Sadau, ta wallafa wannan hoto tare da Adam Zango inda take cewa shi kadai ne "Yariman da na sani" a masana'antar Kannywood. Hakkin mallakar hotoInstagram/adam_a_zangoImage caption ...washegari Adam Zango ya wallafa hotonsa da matarsa, Safiya, yana mai cewa "Daga ke..." ba kowa ko? Hakkin mallakar hotoInstagram/@centurymediaacademyImage caption Ali Nuhu a cikin fim mai suna A Call To Service, wanda aka yi domin wayar da kan masu yi wa kasa hidima a Najeriya Hakkin mallakar hotoInstagram/falalu_a_dorayiImage caption Falalu Doraya (hagu) da Nazifi Asnanic suna tattaunawa. Me suke cewa ne? Hakkin mallakar hotoInstagram/abbaelmustapha1Image caption Abba Almustapha ya wallafa wannan hoto a shafinsa na Intagram ranar Juma'a inda yake godiya ga Allah bisa samun digiri mai daraja ta biyu Hakkin mallakar hotoInstagram/nuhuabdullahiImage caption Mene ne ya yi wa Nuhu Abdullahi dadi, a sanya shi kyakkyalewa da wannan dariya?