Bidiyon na dauke da jaruman biyu cikin yanayi na farin ciki, ya kuma yi kama da hotunan da amarya da ango kan dauka gabanin aure wanda ake kira “pre-wedding pics.
Washington D.C. —A karshen makon da ya gabata ne jaruma Maryam Booth ta wallafa wani bidiyo wanda ya nuna yadda suka caba ado da ita da jarumi Adamu Garba na shirin Labarina, wanda ya fito a matsayin “Raba Gardama.”
Bidiyon na dauke da jaruman biyu cikin yanayi na farin ciki, ya kuma yi kama da hotunan da amarya da ango kan dauka gabanin aure wanda ake kira “pre-wedding pics.”
Kazalika an ga jarumar ta rubuta a kasan bidiyon cewa “Dear Husband” wato “Ya Mijina” hade alamar zuciya da ke nuna soyayya.
Ya zuwa lokacin wallafa wannan labarin, mutum sama da dubu 25 ne suka nuna kauna ko liking ga bidiyo wanda yake dauke da wakar Namenj da ake kira “Gani.”
Wasu daga cikin wadanda suka yi sharhi kan bidiyon sun yi ta yi wa jaruman biyu murnar Allah ya ba da zaman lafiya.
Wasu kuwa sun yi nuni da cewa ba aure za su yi ba fim ne.
A wasu lokuta jarumai kan dauki irin wannan bidiyo ko hoto su yada a shafukansu na sada musamman a lokutan da ake daukan wani fim dan janyo ce-ce-ku-ce.