Lauyan Combs ya ce abokin aikinsa ba shi da laifi kuma ya musanta zarge-zargen ranar Talata.
Washington D.C. —An tuhumi Sean "Diddy" Combs da laifin safarar mutane don karuwanci da kuma zamba a wani bincike da ake ci gaba da gudanarwa a birnin New York.
Muhimman bayanai daga sabuwar tuhumar da aka bude sun hada da bayani kan wasu ayyukan lalata da ake wa lakabi da "Freak Offs" da jami’ai ke cewa Combs ya shirya tsakanin wadanda ake zargin ya cuta da maza da suke sana'ar karuwanci.
Jami’an sun ce fitaccen mawakin hip-hop din ya rika shayar da wadanda ya cuta magunguna saka maye yayin wadannan aika-aika, sannan yana daukar hoton bidiyonsu.
Tuhumar ta kuma zargi Combs da jagorantar wata kungiya ta laifi.
Masu gabatar da kara sun ce shi da abokan aikinsa sun aikata ayyukan laifi da dama, ciki har da safarar mutane don karuwanci, tilasta aiki, tura mata da maza don karuwanci, laifukan miyagun kwayoyi, garkuwa da mutane, kona gida da kuma bayar da cin hanci da hana shari’a yin aiki.
Lauyan Combs ya ce abokin aikinsa ba shi da laifi kuma zai musanta zarge-zargen ranar Talata.