Bikin na ranar Talata ya zo ne kimanin makonni biyu bayan da Davido ya tabbatar da aurensa da Chioma.
WASHINGTON D.C. —A ranar Talata ne aka gudanar da shagalin bikin auren fitaccen mawakin Afrobeat Davido Adeleke da dadaddiyar budurwarsa Chioma Rowland a wani kasaitaccen bikin auren gargajiya a birnin Legas da ya samu halarta ‘yan masana’antar nishadantarwa da wasu manyan baki.
Taron bikin, wanda aka gudanar a Harbor Point da ke yankin Victoria Island a jihar Legas, ya nuna shekarun da suka shafe suna soyayya, kuma kamar yadda ake sa ran bikin ya karade shafukan sada zumunta.
Bikin na ranar Talata ya zo ne kimanin makonni biyu bayan Davido da ya tabbatar da aurensa da Chioma.
Davido Da ChiomaHotunan bikin sun karade shafukan sada zumunta yayin da masoya, fitattun mutane, sarakunan gargajiya da ‘yan siyasa suka taya ma’auratan murna.
Masoya da mashahuran mutane sun yi ta yada hotuna da bidiyo daga bikin, inda su ke taya sabbin ma’auratan murnar auransu.
Kamar yadda aka zata, auren Davido za’a samu halartar manyan baki daga sassan daban-daban na rayuwa.
Davido da ChiomaDaga cikin wasu manyan bakin da suka halarci taron bikin Davido da Chioma sun hada da Ooni of Ife Oba Adeyeye Ougnwusi, Victor Osimhen; tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom Udom Emmanuel; tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo; Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki; da takwarar aikinsa na ona Ogun Dapo Abiodun; Sanata Daisy Danjuma, mai wakiltar Edo ta Kudu.
Abotar Chioma da Davido ta samo asali ne tun shekaru da dama da suka gabata. Amma a shekarar 2018 ne mawaki ya tabbatar da soyayarsu a wani taron jama’a a watan Oktoba na 2018.
Har ila yau Davido ya gwangwaje amaryarsa Chioma da wata sabuwar mota a ranar Talata.