An Tuhumi Mutane 5 Da Laifin Mutuwar Tauraron 'Friends'

An Tuhumi Mutane 5  Da Laifin Mutuwar Tauraron 'Friends'

Wani mai gabatar da kara ya ce an tuhumi wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a mutuwar Matthew Perry sakamakon amfani da wani magani mai hadari da ake kira ketamine a bara, ciki har da mataimakin jarumin da kuma likitoci biyu.

Washington, DC — 

Lauyan gwamnatin Amurka Martin Estrada ne ya sanar da tuhumar a jiya Alhamis, yana mai cewa, likitocin sun ba Perry magani mai yawa na ketamine da har sun nuna shakkun a cikin sakon tes ko nawa tsohon tauraron wasan "Friends" zai yarda ya biya.

Estrada yace "Wadannan da ake tuhuma sun yi amfani da jarabar shan miyagun kwayoyi da Mista Perry ke fama da ita don arzuta kansu. Sun san abin da suke yi bai dace ba."

Perry ya mutu a watan Oktoba saboda yawan ketamine da aka dura masa, kuma mataimakinsa da ke zama tare da shi ya yi mashi allurai da yawa na miyagun kwayoyi a ranar da ya mutu. Mataimakin nashi, Kenneth Iwamasa, shi ne wanda ya iske Perry ya mutu a wannan rana.

Lauyan gwamnati a California , Martin Estrada na jawabi ga manema labarai kan kama mutanen da ake tuhuma da mutuwar Mathew Perry Lauyan gwamnati a California , Martin Estrada na jawabi ga manema labarai kan kama mutanen da ake tuhuma da mutuwar Mathew Perry

Hukumomi sun bayyana cewa, jarumin ya je neman maganin wurin likitocin biyu da aka tuhuma, bayan da likitocinsa suka ki ba shi ketamine da yawa da yake so.

Shugabar Hukumar yaki da miyagun kwayoyi Anne Milgram ta ce wani lokaci, dan wasan ya biya dala 2,000 kan kwalin ketamine wanda daya likitan ya saya dala 12.

An kama biyu daga cikin mutanen, ciki har da daya daga cikin likitocin da ake tuhuma, jiya Alhamis, in ji Estrada. Biyu daga cikin wadanda ake tuhumar, ciki har da Iwamasa, sun amsa laifin da ake tuhumar su da su, kuma mutum na uku ya amince ya amsa laifin.

Furannin karrama marigayi Mathew Perry Furannin karrama marigayi Mathew Perry

Daga cikin wadanda aka kama a jiya, akwai Dr. Salvador Plasencia, wanda ake tuhuma da laifuka bakwai na rarraba ketamine da kuma tuhume-tuhume biyu da suka shafi bada bayanan karya bayan mutuwar Perry.

An kuma kama Jasveen Sangha, wadda masu gabatar da kara suka bayyana a matsayin dillaliyar miyagun kwayoyi da aka fi sani da "Queen ketamine" Maganin Ketamine da Sangha ta kawo ya yi sanadiyar mutuwar Perry, in ji hukumomi.

Mai gabatar da kara ya ce wadanda ake tuhumar sun yi musayar sakonni jim kadan bayan mutuwar Perry suna nuna ketamine a matsayin sanadin mutuwarsa.

Jaruman wasan talabijin "FRIENDS" Jaruman wasan talabijin "FRIENDS"

Perry ya shafe shekaru yana fama da jarabar shan miyagun kwayoyi tun daga zamanin da yake tashe a a wasan talabijin da ake kira "Friends," lokacin da ya zama daya daga cikin manyan taurarun talabijin na zamaninsa.

Mutuwar shahararrun mutane da dalilin ta’amali da miyagun kwayoyi lokutan baya ya sa hukumomi gurfanar da mutanen da suke kawo musu.

Jarumar Kannywood Daso - Saratu GidadoJarumar Kannywood Daso - Saratu Gidado Ku Duba Wannan Ma

Allah Ya Yi Wa Jaruma Daso Saratu Gidado Rasuwa

16x9 Image16x9 Image

Grace Alheri Abdu

Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Subscribe

News Source:   VOA (voahausa.com)