An Tsinci Gawawwakin Jarumin Hollywood Gene Hackman Da Matarsa A Gidansu

An Tsinci Gawawwakin Jarumin Hollywood Gene Hackman Da Matarsa A Gidansu
washington dc — 

A jiya Laraba aka tsinci gawar jarumin masana’antar shirya fina-finan Amurka Gene Hackman a gafen ta matarsa a gidansu.

Hackman mai shekaru 95 da matarsa, Betsy Arakawa mai shekaru 63, sun mutu a gidansu da ke garin New Mexico tare da karensu, inda hukumomi suka shaidawa kafafen yada labarai cewa babu wata alamar rashin gaskiya ko aikata laifi.

Babban jami’in tsaron yankin Santa Fe Adan Mendoza bai bayyana musabbabin mutuwar ma’auratan ba, wadanda suka kasance tare tun shekarar 1991.

Hackman, wanda ya taba lashe kyautar Oscar har sau 2, ya samo yabo a kan rawar da yake takawa a fina-finai masu matukar daukar hankali sakamakon wahalhalun da ya sha yana tasowa, inda sunansa ya bayyana a dimbin fina-finai lokacin da shekarun haihuwarsa suka kai 70.


News Source:   VOA (voahausa.com)