An Kaiwa Jarumin Bollywood Saif Ali Khan Hari A Gidansa

An Kaiwa Jarumin Bollywood Saif Ali Khan Hari A Gidansa
WASHINGTON DC — 

A ranar Alhamis wani mutum ya daddabawa jarumin masana'antar shirya fina-finai ta Bollywood Sif Ali Khan wuka a gidan shi da ke Mumbai.

Sai dai likitocin da ke yi masa magani sunce baya cikin hadari.

Khan mai shekaru 54 na kan warkewa daga wata jinyar ne, inda itama aka caccaka masa wuka a kashin makarkafarsa, da wuyansa da hannu, kamar yadda likitocin suka shaidawa manema labarai.

Daya daga cikin likitocin da su ka yiwa Khan tiyata Dr Nitin Dange, yace, jarumin ya samu mummunan rauni a kashin gadon bayansa, inda daga bisani aka yi masa tiyata aka cire wukar da ta kafe a cikin kashin, da gyara masa inda bargon kashinsa ya rika yoyo.

Mutumin wanda ya balla kofa ya shiga gidan, ya dabawa Khan wuka ne, a lokacin da Khan din ya yi kokarin hana shi shiga gidan, a unguwarsu da ke Bandra a birnin Mumbai, a cewar yansanda da kafafen yada labaran kasar.


News Source:   VOA (voahausa.com)