An Kafa Tarihin Nada Dan Kabilar Igbo Limami A Masallacin Kasa Na Abuja

An Kafa Tarihin Nada Dan Kabilar Igbo Limami A Masallacin Kasa Na Abuja

A wani babban al’amarin da ya shafi al’ummar Musulmin Najeriya, an nada Farfesa Ilyasu Usman, dan kabilar Igbo na farko, a matsayin limamin masallacin kasa na Abuja.

washignton dc — 

Yau ta kasance muhimmiyar ranar da sabon limamin ya gabatar da hudubarsa ta sallar Juma’a, matakin da ya zamo abin alfahari ga Musulmin Najeriya baki-daya.

Farfesa Ilyasu Usman Farfesa Ilyasu Usman

Hukumar gudanarwar babban masallacin kasa na Abuja ta gano tarin gudunmowar da Farfesa Usman ya baiwa ilimin addinin Musulunci, kuma ana ganin nadin nasa a matsayin wata nasara wajen kara hadin kan al’ummar Musulmi.

Kungiyar Musulmi ‘yan asalin yankin kudu maso gabashin Najeriya (SEMON) ta yi maraba da wannan shawara, inda ta yabawa nadin nasa a matsayin manuniya ga irin gudunmowar daya bayar wajen hidimtawa addinin Musulunci da harkokin jagorancinsa.


News Source:   VOA (voahausa.com)