Shahararrun ‘yan kasuwa na duniya da ‘yan siyasa sun fara hallara babban birnin kasar India a ranar Juma’a domin halartar daurin auren karamin dan Mukesh Ambani, wanda ya fi kowa arziki a Asiya.
WASHINGTON, D. C. —Anant Ambani, mai shekaru 29, ya auri budurwarsa da ta dade suna tare Radhika Merchant, a wani abu da mutane da yawa suka kira gagarumin bikin aure na shekara.
Liyafar sa albarka ga ma’auratanBikin na gudana ne a cibiyar taron Jio World Convention Centre mallakar Ambani da ke Mumbai da kuma gidan danginsu.
Biki ne da aka kwashe watanni ana shirye-shirye na bukukuwan aure da ke dauke da wakoki daga fitattun jarumai ciki har da Rihanna da Justin Bieber.
Baki da suka halarta lokacin bikin Anant AmbaniAn dai fara bikin na kwana hudu ne da bikin daurin auren na Hindu a ranar Juma'a, sannan za a yi gagarumar liyafa a karshen mako.
Jerin baki da suka halarci bikin dai ya hada da tsohon Firaministan Burtaniya Tony Blair da Boris Johnson da Shugaban Kamfanin Saudi Aramco Amin H. Nasser da Adele da Lana Del Rey da Drake da David Beckham, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka bayyana.
Bikin ‘dan shahararran mai kudi a AsiyaTashoshin labarai na Talabijin sun kuma nuna mashahuran mutane kamar Kim Kardashian da ƙwararren ɗan kokawa da ɗan wasan Hollywood John Cena sun isa wurin bikin.
-AP