Bayanai daga sassan ƙasar gami da hotunan dake yawo a shafukan intanet sun nuna yadda matasa suka fara fitowa, yayin da a wasu wuraren aka samu jinkirin fitar ɗangon da ake dakon gani.
Wannan na zuwa ne duk da jerin matakan sassauta tsananin da ake ciki da gwamnatin Najeriyar da ɗauka domin rarrashin ‘yan ƙasar ciki har da shirin fara sayar da buhun shinkafa mai kilo 50 akan naira dubu 40 a maimakon kusan naira dubu 80.
Ko a jiya Laraba sai da Majalisar Dattijan Najeriya ta bakin shugabancta Godswill Akpabio ta roƙi ‘yan ƙasar da su yi haƙuri su bai wa shugaba Bola Ahmad Tinubu ƙarin lokaci wajen aiwatar da matakan da za su kawo ƙarshen matsin rayuwar da ake ciki.
Kwamarade Bello Basi Fagge, mai fashin baƙi kuma ɗan gwagwarmaya a Najeriya, yayi tsokaci kan dalilin da ya sa gwamnati gaza dakatar da zanga-zangar
01:08Kwamarde Bello Basi Fagge kan dalilan da yasa masu zanga-zanga suka ƙi sauraren gwamnati
Masu zanga-zangar dai sun sha alwashin shafe kwanaki 10 suna fita jerin gwano don bayyanawa gwamnati halin da ake ciki gami da yin kiran da ta gaggauta janye wasu manufofi da take aiwatarwa.
A jiya Laraba ne dai kotuna a wasu jihohin Najeriya suka taƙaita wuraren da masu zanga-zanga za su yi wa dafifi, inda suka haramta musu taruwa a wasu wuraren da dama.
Jihohin da kotuna suka bayar da umarnin taƙaita kai kawon masu zanga-zanga kan tsadar rayuwar dai sun haɗa da Legas, Kwara, Ogun da kuma birnin Abuja, umarnin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sha alwashin tabbatar da an yi masa biyayya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI