Matsalar dai ta samo asali ne tun lokacin da aka yi juyin mulki a ƙasar, inda ƙasashe makota da suka hada da Najeriya da Benin suka rufe iyakokinsu, saboda haka ala dole dillalan shinkafar ke sauke ta a tashar jiragen ruwan birnin Lome da ke Togo, lamarin da ya ruɓanya nisan hanyar da ake amfani da ita domin isar da shinkafar cikin Nijar.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoton Michael Kuduson
Tun ana korafi game da hauhawar farashin shinkafa da ta kasance abincin da aka fi ci a kasar, a yanzu dai ta kai inda za a ce jama'a sun dangana tare da neman sauki daga Allah.
Wani magidanci, Amadu Rufa'i titin bugaje, cewa ya yi, bai taba ganin yanayi irin wannan ba a rayuwarsa.
A Nijar, jama'ar da dama ne ke mamakin yadda farashin ke ta hauhawa, wata alama da ke nuni da cewa an sakar wa ‘yan kasuwa ragama domin kayyade farashin.
Akwai dalilai da dama da ke haddasa wannan matsala, domin tun bayan juyin mulkin soji suka yi a kasar, wasu ‘yan kasuwar suka daina odar shinkafar daga ketare, to amma duk da haka akwai wadanda ke ci gaba da sana’ar har ma suka samu yabo daga gwamnati.
A watan Fabrairun da ya gabata ne gwamnatin Nijar, ta sanar da kayyade farashin shinkafa a duk fadin kasar, amma ga alama mafi yawan ‘yan kasuwa sun ki mutunta matakin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI