Kungiyar ta ce ta kai hari ne domin neman ganin an saki hambararren shugaban kasar Mohmed Bazoum.
Wannan dai sabuwar kungiya ce da ke karkashin jagorancin wani mai suna Mahamat Tori, wadda ta sha bamban da kungiyar FPL da Mahmoud Salah ke jagoranta, wadda ta fasa bututun man fetur da ke sada Nijar da Jamhuriyar Benin a ranar 16 ga wannan wata na Yuni da muke ciki.
'Yan bindigar sun yi wa kantoman na Bilma da ke cikin jihar Agadez da kuma tawagarsa kwanton bauna ne, a lokacin da suke dawowa daga wani taro a garin Dirkou da ke gabashin Agadez kusa da iyaka da Libya, inda bayanai ke cewa biyu daga cikin jami’an tsaron da ke yi musu rakiya sun rasa rayukansu a lamarin.
Shugaban gundumar ta Bilma wanda shi kansa jami’in tsaro ne wato Kwamanda Amadou Torda, da shugaban rundunar jami’an tsaron Jandarma da kuma wasu jami’an tsaro 3 ne ke ci gaba da kasancewa a hannun ‘yan bindigar.
A sanarwar da ta fitar kwana daya bayan faruwar lamarin, ma’aikatar tsaron cikin gidan kasar Nijar ta ce tabbas wasu ‘yan bindiga sun kai hari kusa da garin Bilma inda suka yi awun gaba da mutane biyar, duk da cewa sanarwar ba ta ambaci sunaye ko mukaman wadanda ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI