Tchiani ya jinjina wa ƴan Nijar shekara guda bayan juyin mulki

Tchiani ya jinjina wa ƴan Nijar shekara guda bayan juyin mulki

 A jawabin nasa, shugaban ya ce tabbas a wannan lokacin akwai barazana da kasar  ke fuskanta na ta’addanci duk da wasu yarjejeniyoyi na baiwa ƙasashen ketare damar kafa sansanonin soji a cikin ƙasar.

Shugaban sojin ya ce almubazzaranci, keta dokokin ƙasa da nuna halin ko in kula na daga cikin abubuwan da tsohuwar gwamnatin ƙasar ta aikata a maimakon muhimmanta dimokuradiyya da take ta nanatawa a  koda yaushe da zummar tallata kanta a idon ƙasashen duniya.

Ganin halin da kasar ta shiga, al’ummar Nijar sun rungumi sabuwar tafiya a karkashin wannan sabon tsari na majalisar sojin ƙasar da ta kifar da gwamnatin farar hular, matakin da wasu daga cikin ƙungiyoyi irin su ECOWAS daukar mataki na ladabtarwa a kan Nijar.

Tchiani ya ce a cikin gida, wannan sauyi ya sa jama’a gano cewa ya dace su rugumi sauyi a fuskoki da dama, kamar ta fuskar shugabanci cikin mutunci ba tare da zancen bawa da ubangida ba.

Shugaban ya ce wannan fata ce na ɗaukacin ƴan kasar da murya guda, yayin da ya ƙara musu kwarin gwiwa a ƙarkashin shugabancin majalisar soji da yake jagorantar ɗaukar nauyin sake gina wannan ƙasa da kuma shimfida sabuwar dangantaka da ta kai ga samar da ƙungiyar kasashen yankin Sahel da makwabtansu na kusa.

Tchini ya ce wasu daga cikin manyan ayyukan da suka saka a gaba a Nijar sun kasance guda hudu kamar haka:

- Tabbatar da samar da tsaro tare da haɗin kai

- Tafiyar da shugabanci bisa tsari na adalci

- Inganta sashen samar da ci gaba.

- Sai na karshe sashen tabbatar da jin kai a cikin ƙasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)