Shugaba Abdourahamane Tiani ya zargi Faransa da son tada zaune tsaye a Nijar

Shugaba Abdourahamane Tiani ya zargi Faransa da son tada zaune tsaye a Nijar

Shugaba Abdourahamane Tiani , a bukin cika shekaru 64 da samun incin kai,ya tattaunawa da dan jarida na tashar tallabijen na gwamnati kan wasu daga cikin matsaloli da ake fuskanta tun bayan ficewa dakarun Faransa daga Nijar.

Shugaba Abdourahamane Tiani ya ce Nijar ta sake kulla kawancen da kasashen duniya,ya na mai cewa tabbas a karshen shekarar da ta gabata ta bukaci Faransa da ta yi mulkin mallaka da ta janye sojojinta da ke yankin Sahel, Shugaban majalisar sojin ta Nijar ya na mai cewa Farnsa ta mayar da sojojinta  a Najeriya da Benin.

Shugaban Majalisar Sojin NIjar a tattaunawa da dan Jarida Shugaban Majalisar Sojin NIjar a tattaunawa da dan Jarida © Capture d'écran du Facebook live de la télévision nationale du Niger

Kasar ta Nijar dai na zargin makwabciyarta Benin a kai a kai da bada dama ga Faransa na girke sojojinta a sansanoni wanda hukumomin Benin da Faransa ke musantawa. Wadannan zarge-zarge dai sun kasance tushen takaddamar diflomasiyya na tsawon watanni da kasar Benin, wadda ta yi kaurin suna wajen kakabawa Nijar takunkumin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta kakaba mata bayan juyin mulkin.

Janar  Abdourahamane Tiani Janar Abdourahamane Tiani © ORTN

 Duk da dage takunkumin da aka kakaba mata a watan Fabrairu, hukumomin Nijar sun ki sake bude kan iyakar kasar da Benin.

A karshe,Shugaba Abdourahamane Tiani ya na mai cewa "Ranar da muka san cewa babu wata barazana daga Benin, za mu dauki matakan da suka dace" don sake bude iyakar kasar mu da Benin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)