Ma’aikatar Kula da Ma’adinan Ƙarƙashin Ƙasa ta Nijar ce ta sanar da kamfanin GoviEx na Canada cewa, daga yanzu ba shi da wani sauran izinin ci gaba da haƙar ma’adinan a garin Madaouela wanda yanzu ke ƙarƙasshin mallakin al’ummma.
Kamfanin na GoviEx ne ya sanar da matakin da gwamnatin Nijar ta ɗauka a kansa a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Alhamis.
Sai dai kamfanin ya ce, yana da ƴancin da zai ba shi damar ƙalubalantar matakin soke lasisinsa na haƙar ma’adinan a gabann kwararrun kotunan cikin gida da na ƙasa da ƙasa.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin na GoviEX ke ƙoƙarin ƙarɓar bashin dala miliyan 200 domin gudanar da gagarumin aikinsa a Madaouela.
Shi ma kamfanin Orano ya yi ƙorafi a ranar 20 ga watan Yuni kan abin da gwamnatin sojin Nijar ta yi masa na soke masa lasisin haƙar ma’adinai a reshensa na Imouraren.
Jamhuriyar Nijar dai na da arzikin mafi kyawun ma’adinin Uranium a nahiyar Afrika, kuma ita ce ƙasa ta bakwai a jerin ƙasashen da ke kan gaba wajen samar da uranium a faɗin duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI