Nijar ta soke lasisin kamfanin Faransa mai haƙar uranium Orano

Nijar ta soke lasisin kamfanin Faransa mai haƙar uranium Orano

Cikin wata sanarwa da ya fitar kamfanin na Orano, ya ce gwamnatin Nijar ta ɗauki matakin soke lasisin nasa ne duk da cewa ya riga ya fara gudanar da ayyuka a filin haƙar makamashin na Uranium da ke arewacin ƙasar daga ranar 12 ga watan nan na Yuni, bayan da ya cika dukkanin sharuɗɗan da mahukunta suka gindaya.

Jim kaɗan bayan juyin mulkin da suka yi a shekarar bara,  sojojin Nijar suka sha alwashin sake nazarin yarjeniyoyin haƙar ma’adanan da aka baiwa kamfanoni a faɗin ƙasar, kan haka ne kuma suka yi gargaɗin kwace lasisin haƙar Uranium a katafaren filin na Imouraren, muddin ayyukan Orano basu kankama cikinsa ba daga ranar 19 ga watan Yunin nan.

Kididdigar ƙwararru dai ta nuna cewar akwai makamashin Uranium kimanin tan dubu 200 shimfiɗe a ƙarƙashin filin haƙar ma’adanai na Imouraren.

A shekarar 2022, Nijar ce ta samar da kashi 1 bisa 4 na adadin makamashin Uranium ɗin da cibiyoyin Nukiliyar kasashen Turai suka yi amfani da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)