Cikin Sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar ta karanta ta gidan talabijin na kasar ta ce Hadin gwiwar kungiyoyin 'yan ta'adda" sun kai wa jami'an tsaro hari a kusa da kauyen Tassia, inda suka kashe sojoji 20 da jikkata wasu 9.
Sanarwar ta ce an jami’an tsaro sun kashe mahara da dama, kuma an tura sojoji ta sama da ta kasa domin zakulo sauran maharan.
Tassia na yankin Tillaberi da ke iyaka da Mali da Burkina Faso inda 'yan tawaye masu alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS suka kwashe kusan shekaru goma suna tada kayar baya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI