A cewar sanarwar da shugaban ƙungiyar Mahamoud Sallah ya fitar, harin da suka kai kan bututun man, na a matsayin gargadi na farko ne ga gwamnatin sojin Nijar, da ke ci gaba da tsare Bazoum.
Ya ce babban burin da suka sanya a gaba shi ne ganin kamfanin hakar mai na China a kasar WAPCO ya dakatar da shirinsa na bai wa gwamnatin sojin Nijar rancen dala miliyan dari 4, inda ya ce matukar hakarsu bata cimma ruwa ba, babu abin da zai hana su gurgunta lamura a cibiyoyin man kasar.
Haka nan kungiyar ta FPL ta ɗauki alhakin harin da ya hallaka sojojin Nijar da ke aikin tsaron bututun mai, wanda shi ne na farko a tarihi da aka taba kai irinsa a kasar.
A dai watan Agustan shekarar da ta gabata ne aka samar da kungiyar ta FPL, bayan da sojoji suka yi wa shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki a ranar 26 ga watan Yulin shekarar bara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI