Mahukuntan Nijar na zargin Bazoum da laifin cin amanar ƙasar, ɗaukar nauyin ta’addanci da kitsa yi wa ƙasar zagon ƙasa, zarge-zargen da makusantansa suka bayyana a matsayin bita-da-ƙulli.
Gwamnatin sojin Nijar na tsare da Bazoum tare da mai ɗakinsa, Hadiza tun bayan hamɓarar da shi daga karagar mulki a ranar 26 ga watan Yuli.
Bayan zaman kotun na wannan Juma’a, ɗaya daga cikin lauyoyinsa, Ould Salem Mohamed ya ce su na nazari a kan hukuncin, kuma za su mayar da martani ta cikin wata sanarwa nan gaba.
Jagororin gwamnatin sojin Nijar na zargin Bazoum da ganawa da shugaban Faransa, Emmanuel Macron da sakataren tsaron Amurka, Antony Blinken ta wayar tarho, inda aka ce ya nemi taimakon soji daga gare su.
Sau biyu ake ɗaga zaman wannan kotu, inda lauyoyin Bazoum suka yi ta ƙorafi a kan shamaki da dama a game da ƙoƙarin su na bai wa hamɓararren shugaban kariya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI