Ko ina aka kwana a yunƙurin sulhunta Benin da Nijar ?

Ko ina aka kwana a yunƙurin sulhunta Benin da Nijar ?

Idan dai za’a iya tunawa, a ranar 24 ga  watan Yuni, tsoffin shugabanin biyu, suka sauƙa a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar, inda suka gana da shugaban gwamnatin rikon kwarya Janar Abdouirahmane Tchiani kafin daga bisani su tattauna da manyan jami’ai da dama ciki harda tsaffin shugabanin kasar.

Dalilin ziyarar

Babbar makasudin ziyarar tsoffin Shagabannin Benin biyu Boni Yayi da Nicephore Soglo, shine kashe wutar ta taso tsakanin kasashen biyu, wanda ya samo asali bayan tsarewa tare da kai wa gidan kaso tawagar wasu ‘yan kasar ta Nijar su 5 ma’aikatan WAPCO wani rashen kamfanin kasar China CNPC ranar 5 ga wanan watan nan na Yuni wadanda suka zo aikin sanya ido kan dakon man fetur din kasar  da za’ayi jigilar sa ta hanyar bututun man da ya ratsa kasar Benin domin yin  kasuwancin sa a ketare kamar yadda yake bayyane a yarjejeniyar da kasahen biyu suka cimma.

Rufe iyakar Nijar

Tun daga wancen lokacin, mahukuntan Nijar suka ɗauki matakin rufe rijiyoyin da ke kai man zuwa bututun da ya hada Nijar da ƙasar Benin, kuma tun kafin wannan lokaci humomin sojin Nijar sun cigaba da barin iyakokin kasashen biyu a rufe.

Kuma har zuwa lokacin kammala wanan  ziyarar, babu wata sanarwa a hukumance da aka fitar daga bangaren gwamatin Nijar ko kuma banagare su tsoffin shugabannin na Benin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)