Jawabin Janar Tchiani bai tabo batun mika mulki ga fara hula ba a Nijar

Jawabin Janar Tchiani bai tabo batun mika mulki ga fara hula ba a Nijar

Kasar wadda a halin yanzu ke karkashin ikon Sojoji  bayan kifar da mulkin zababen Shugaban kasa Bazoum Mohamed a watan Yulin shekara bara, na cigaba da nuna turjiya ga manufofin kasashen yammacin duniya .

Wani abu dake nuni karara sabuwa alqiblar  da sabbin mahukuntan  suka dosa ,shi ne yadda Shugaban mulkin sojin kasar Birgedia Janar Abdurahamane Tchiani yaki dauko batun mika mulki ga fara hula cikin jawabin sa ga ‘yan Kasar a jajibirin  rana bikin cika kasar shekaru 64 da samun ‘yancin kai.

Wanan batu dai ya janyo shan suka da martani daga ‘yan kasar da kuma ‘yan siyasa.

Sahanounou Mahamadou, tsofan mai baiwa Bazoum Mohamed shawara kan harakokin zamantakewa ya yi tsokaci akai.

Ku latsa alamar sauti domin sauraron karin bayani.....

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)