Bayan shekara guda da juyin mulkin da sojojin Nijar suka yi wa Mohamed Bazoum, shugaban gwamnatin mulkin sojin kasar Abdourahamane Tiani da firaministansa Ali Mahamane Lamine Zeine na ci gaba da taka rawar gani wajen ceto tattalin arzikin kasar da kuma kokari wajen gina sabuwar diflomasiyya da kasashen duniya.
Bayan wannan tsawon lokaci da hambararren shugaban kasar ta Nijar Bazoum ya shafe ba tare da ya shaƙi iskar ƴanci ba, kar ya zuwa yanzu yana nan a tsare a hannun sojin kasar ba tare da an sake shi ba.
A ranar 14 ga watan Yuni ne kotun shari’ar da gwamnatin mulkin sojan kasar ta kafa ta maye gurbin wadda ke zamanta a birnin Nyame, a yayin da ta cire duk wata kariyar da doka ta bashi, wanda hakan ya baiwa kotun sojin ci gaba da sauraron shari.arsa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI