Halin da ƴan gudun hijira ke ciki a Diffa na Nijar

Halin da ƴan gudun hijira ke ciki a Diffa na Nijar

A jihar Diffa da ke Jamhuriyar Nijar kawai, yanzu haka akwai sama da mutane dubu 143 da ke rayuwa a matsayin ƴan gudun hijira. 

Ku latsa alamar sauti domin sauraren cikakken rahoton Michael Kuduson.

Tun a 2015 aka fara samun ƴan gudun hijira a Diffa, bayan da ayyukan Boko Haram suka tsananta a Najeriya tare da tilasta wa jama’a tserewa zuwa Nijar. 

Mafi yawan ƴan gudun hijirar sun dogara ƙungiyoyin agaji ne domin samun abinci da kuma matsugunai. 

Lura da cewa mafi yawan ƴan gudun hijirar sun share tsawon shekaru zaune a cikin sansani, wannan ne ya sa ƙungiyoyin agaji da kuma mahukunta a Nijar suka ɓullo da tsari na musamman don koya musu sana’o’i.

Bikin na shekarar bana na zuwa ne a daidai lokacin da duniya ke fama da yake-yake, da suka hada da Sudan, Gaza da kuma Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)