Gwanmatin sojin Nijar ta tabbatar da zagon ƙasa a bututun mai a Benin

Gwanmatin sojin Nijar ta tabbatar da zagon ƙasa a bututun mai a Benin

A daren ranar 16 zuwa 17 ga watan Yuni ne, aka fasa wani bangare na bututun man, kamar yadda gidan talabijin na Tele Sahel ya rawaito da yammacin jiya Juma'a.

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne ƙungiyar ‘yan tawayen Patriotic Liberation Front da ke fafutukar ganin an sako shugaba Mohamed Bazoum, ta ce ta fasa bututun ne a matsayin sako ga hafsoshin sojin Nijar.

Shugaban ƙungiyar ƴan tawayen, Mahamoud Sallah ya buƙaci a sako hamɓararren shugaban, ko kuma su kai hari rijiyoyin man ƙasar. 

A ranar 26 ga watan Yuli aka wayi gari da labarin cewar sojojin da suke tsaron fadar shugaban kasa, a karkashin jagorancin Janar Abderahmane Tchiane sun tsare shugaba Bazoum a cikin fadarsa, abinda ya jefa fargaba a ciki da wajen kasar. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)