A wata sanarwa da ta fitar a mujallarta da ke kawo rahoton ayyukanta na mako-mako, rundunar sojin ta ce wani haɗin gwiwar dakarunta na ci gaba da kisan ƴan ta’addar da suka kashe mata sojoji 20 a harin yankin Tera, wanda ayyukan yan ta’adda masu ikirarin jihadi suka yi wa dabaibayi.
A cikin wata sanarwa ta dabam, rundunar sojin ta ce ko bayan harin naTera, sai da ta kashe wani jagoran ƙungiyar IS a yankin tare da mayaƙansa akalla 30, kwana guda bayan da ƴan b ta’adda suka salwanta mata sojoji.
Garin Tera dai yana yankin Tillaberi ne, mai iyaka da ƙasashen Burkina Faso da Mali, inda mayaƙa masu alaƙa da ƙungiyar al-Qaeda da IS da ke ikirarin jihadi suka shafe shekaru kusan 10 su na cin karensu babu babbaka.
A wannan yankin, mayaƙa masu ikirarin jihadin su na yawan kai wa farare hula hare-hare, lamarin da ya sa ɗimbin al’umma yankin ke barin gidajensu.
Wannan yanki na yammacin Jamhuriyar Nijar ya daɗe yana fama da hare-haren ƴan ta’adda masu ikirarin jihadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI