Babu zancen ECOWAS a wannan tafiyar-Janar Abdourahamane Tiani

Babu zancen ECOWAS a wannan tafiyar-Janar Abdourahamane Tiani

Kawancen kasashen Sahel na gudanar da wannan taro ne a wani lokaci da kungiyar kasashen yammacin Sahel wato ECOWAS ta shirya wani taro a Abuja dake birnin Tarraya a Najeriya.

Ibrahim Traoré na Burkina Faso da  Assimi Goïta na Mali da Janar  Abdourahamane Tiani. Ibrahim Traoré na Burkina Faso da Assimi Goïta na Mali da Janar Abdourahamane Tiani. © Olympia de Maismont / AFP / France 24 / RTN / Montage RFI

Rahotanni daga fadar shugaban kasar Burkinabe, "yakin da ta'addanci" da "karfafa dangantakar hadin gwiwa" na daga cikin zantukan da shugabanin uku za su yi Magana a kai.

Shugaban majalisar sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tiani ya bayyana cewa,yanzu kam kasashen yankin da suka hada da Nijar,Burkina Faso da Mali sun rungumi salon dafawa juna a fanoni da suka hada da tsaro,kiwon lafiya .diflomasiya da batun yaki da ta'addanci.

Janar Abdourahamane Tiani da shugaban majalisar sojin Burkina Faso Ibrahim Traore Janar Abdourahamane Tiani da shugaban majalisar sojin Burkina Faso Ibrahim Traore AFP - -

Janar Abdourahamane Tiani ya na mai jadadda kira da cewa kofar wannan hadaka ta su a bude ta ke ga duk kasar dake bukatar kasancewa da su domin babu zancen Ecowas yanzu kam.

A wannan  taro shugabanin kasashen na sa ran cimma mataki da za ya kai su ga samar da tsari na dukulallen yanki mai cin gashin kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)