A makon da ya gabata kamfanin na Orano ya ce an kawar da shi daga filin haƙar uranium na yankin Imouraren a arewacin Nijar, a wani mataki da ke nuni da tankiya tsakanin Faransa da gwamnatin sojin ƙasar da ke yammacin nahiyar Afrika.
Gwamnatin ba ta mayar da martani ba kafin ta fitar da wata sanarwa a ranar Litinin, wadda ke cewa filin haƙar uranium na Imouraren ya koma ƙarƙashin ikon gwamnati.
Gwamnatin ta kare kanta a game da soke lasisin Orano, tana mai cewa kamfanin ba ya mutunta yarjejeniyar da aka ƙulla da shi duk kuwa da tunatarwa har sau biyu da aka yi masa daga ma’aikatar kula da haƙar ma’adinai a watan Fabrairun 2022 da Maris na wannan shekarar.
Kamfanin Orano ya ce a shirye ya ke ya shiga tattaunawa da mahukuntan Nijar, kuma yana da damar ƙalubalantar matakin su a kotu.
Akwai kimanin tan dubu dari 2 na ƙarfen uranium, wanda ake amfani da shi wajen kirar makamai a wannan mahaƙa ta Imouraren.
Amma an dakatar da aiki a wurin biyo bayan faɗuwar farashin uranium a duniya, wadda ta biyo bayan hatsarin nukiliya a shekarar 2011 a Fukushima na Japan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI