Ma’aikata cikin gidan ta ce maharan a kan babura biyu, sun yi wa ayarin da ke ɗauke da prefect na birnin Bilma kwaton ɓauna ne a lokacin da ya ke dawowa daga wani aiki.
Daya daga cikin mutanen da ke cikin ayarin ya mutu a harn da ya auku a wani yanki mai nisan kilomita 17 daga arewacin Bilma, kana daya ya samu mummunan rauni, sannan aka yi awon gaba da mutane biyar.
Sanarwar ba ta bayyana sunayen waɗanda aka yi garkuwa da su ba, amma rahotanni sun ce prefect na Bilma, Amadou Torda na daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI