Za mu sake fasalin taimakawa 'yan gudun hijira - MDD

Za mu sake fasalin taimakawa 'yan gudun hijira - MDD

Daraktan ayyukan hukumar, Raouf Mazou ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci tawaga zuwa Najeriya domin ganawa da hukumomin kasar.

Bayan jinjinawa Najeriya a kan matakan da take dauka musamman daga garuruwan da suka tsugunar da wadanda suka tsere daga muhallinsu, Mazou ya shaidawa mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima cewar za su karbo kudaden da Bankin duniya ya ware domin taimakawa irin wadannan mutane domin ganin sun ci gajiyarsa a Najeriya.

Mataimain shugaban Najeriya Kashim Shettima da Raouf Mazou, Daraktan UNHCR Mataimain shugaban Najeriya Kashim Shettima da Raouf Mazou, Daraktan UNHCR © Nigeria Prtesidency

Daraktan ya ce sabon tsarin na su zai kaucewa bada tallafi zuwa daukar matakan da za'a inganta rayuwar irin wadannan mutane domin ganin sun tsaya da kafafuwansu.

Mazou yace akwai wasu 'yan Najeriya dake gudun hijira a kasashen dake makotaka da kasar, kuma sun bayyana aniyarsu ta dawowa gida ta kashin kan su, saboda haka za'a taimaka musu.

Daraktan yace babu hannun su wajen tilastawa irin wadannan mutane komawa gid aba tare da son ran su ba.

Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima © Nigeria Presidency

A na shi jawabi, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya shaidawa tawagar cewar gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu za ta bai wa kungiyoyin bada agaji da abokan hulda na kasashen duniya hadin kan da suke bukata domin ragewa mutanen da suka tsere daga muhallin su radadin halin da suka samu kan su.

Shettima ya yabawa Majalisar dinkin duniya a saboda irin taimakon da take bai wa Najeriya a shekarun da suka gabata musamman a yankin arewa maso gabas, ya yin da ya musu alkawarin cewar gwamnatin kasar za ta ci gaba da hada kai da duk masu ruwa da tsaki domin tallafawa mutanen dake bukatar taimako sakamakon tashin hankali ko kuma wadanda wani iftila'i da ya abka musu.

Mataimakin shugaban ya ce kofar su a bude take ko yaushe domin hadin kai da aiwatar da sabbin dabarun inganta rayuwar jama'ar kasar da kuma sake tsugunar da wadanda suka bar gidajen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)