Za mu kori mabarata daga Abuja - Minista Wike

Za mu kori mabarata daga Abuja - Minista Wike

Wike ya ce sannun a hankali birnin Abuja na komawa wani dandalin mabarata, kuma gwamnati ba zata aminta da haka, saboda haka zata dauki mataki a kai.

Ministan ya shaidawa mazauan birnin cewar idan sun san suna da 'yan uwa mabarata to su gaggauta daukar mataki a kan su, ko kuma gwamnati ta kwashe su a kan tituna.

Wike yace abin takaici shi ne baki da zaran sun ziyarci birnin, abinda suke fara karo da shi shine mabaratan a kan tituna, matakin da ya ce gwamnati ba zata laminta da shi ba a yunkurin ta na daga darajar birnin kamar takwarorinsa dake kasashen duniya.

Ministan ya ce hakkinsu ne su mayar da birnin Abuja matakin da zai yi gogayya da irinsa dake kasashen duniya, saboda haka ba za su kauda kan su suna ganin mabarata na mamaye birnin ba.

Matsalar bara na daga cikin manyan kalubalen da ke fuskantar gwamnatoci a manyan biranen Najeriya da kuma Abuja, sai dai masana tatatlin arziki na danganta yawaitarsu da karyewar tattalin arzikin Najeriya da matsalar rashin tsaron da ta raba manoma da 'yan kasuwa daga sana'oin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)