Wannan na ƙunshe a wani gargaɗi da hukumar kula da albarkatun ƙasar NMDPRA ta yi.
Hukumar ta zargi cewar da yawan gidajen mai mallakin yan kasuwa sun ƙara farashi zuwa 900 ko ma 1000 kan kowacce lita.
Hakan ya sa alumma kokawa kan yaddda aka samu bambanci tsakanin farashin a gidajen mai na ƴan kasuwa da na kamfanin mai na ƙasar NNPCL, inda a nan ake sayar da kowacce lita kan naira 567 zuwa naira 617 abinda ya haddasa dogayen layuka a gidajen.
Dillalan man fetur na sun yi wuƙar ƙugu da cewar dalilin da ya sa suka ƙara farashin shine saboda yadda suke saro man da tsada daga a defon yan kasuwa, inda yake kaiwa Naira 850 kowaccce lita.
Mai magana da yawun hukumar kula da albarkatun ƙasa a Najeriya Geoge Ene-Ita ya musanta wannan ikirari na ƴan kasuwar. Ya ce sun sanya jami’ansu suna bada bayanan farashi a defo-defo kowacce rana kuma bai kai Naira 850 kan kowaccce lita.
Da aka nuna masa rahotannin yadda wasu gidajen mai ke sayar da kowacce lita kan dubu 1 ya, Ene Ita ya ce zasu garƙame irin waɗanann gidajen man zarar suka kama su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI