Za mu fara aikin gyara lantarkin arewacin Najeriya yau Alhamis –TCN

Za mu fara aikin gyara lantarkin arewacin Najeriya yau Alhamis –TCN

Wannan ya biyo bayan yadda jami’an hukumar suka ce sun gano wata tangardar da aka samu a babbar tashar rarraba lantarki ta Ugwuji-Apir.

Kamfanin ya tabbatar da ɗaukewar lantarki a sassan arewacin Najeriya bayan sauƙar layin wuta na daya da na biyu na Ugwaji Apir abinda ya jefa damuwa ga alummar yankin.

Babban jami’in dake kula da matsalolin jama’a na kamfanin Ndidi Mbah ya ce sun gano matsalar a yankin Igumale na jihar Benue.

Ya ƙara da cewa tuni kamfanin TCN ya fara shirye-shirye da tattara kayan aiki da ake da buƙata domin fara gyara wannan matsala a yau Alhamis.

Tunda farko TCN ya tura tawagar ƙwararru guda 2 domin gano matsalar da ta janyo ɗaukewar lantarkin arewacin Najeiya sai dai ba su samu nasara ba har sai zuwa yammacin ranar laraba.

Batun ɗaukewar lantarki a Najeriya ya zama babban abin tatttaunawa saboda saukar manyan turakun lantarki da ake ta samu babu ƙaƙƙautawa a baya-bayannan.

Matsalar ta jefa masu sana’o’in dake amfani da lantarki da jama’ar yankin arewacin ƙasar da lamarin ya fi ƙamari cikin tsaka mai wuya, abinda ya sa suke ta korafe-ƙorafen ganin an gyara lantarkin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)