Wasu majiyoyi sun bayyana cewa tsananin yunwar na barazana ga ƙoƙarin da ake na yaƙar ɓurɓushin ta’addancin da ya rage a jihohin yankin.
Tun a shekarar 2009 jihar Borno ta yankin na arewa maso gabashin Najeriya ta fara fama da matsalolin tsaro daga ƙungiyar Boko Haram ko da ya ke an yi nasarar murƙushe ƙungiyar a 2016 in banda ɓurɓushinta da ya rage, sai dai ƙungiyoyin agajin irin WFP na ganin matsananciyar yunwa da ƙuncin rayuwa baya ga talaucin da ke damun al’ummar yankin ka iya taso da ƙungiyoyin tayar da ƙayar baya.
Babbar daraktar shirin abinci na Majalisar ɗinkin duniyar WFP Cindy McCain yayin ziyarar da ta kai Damasak guda cikin yankunan da ta’addancin boko haram ya tagayyara ta ce ta ganewa idonta matsananciyar uƙubar da jama’a ke ciki.
Baya ga jihar Borno jihohin Adamawa da Taraba da Yobe na sahun waɗanda ke fama da ƙamfar abinci baya ga tsadar rayuwa lura da yadda ƙarin farashin man fetur ya fi shafarsu fiye da ko'ina a Najeriyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI