Jaridar Premium Times ta ce sabon jirgin ya isa Abuja ne daren jiya, bayan kamfanin China da ya sa kotu ta kwace shi ya amince a saki guda da zai kai shugaba Tunubu Faransa.
Jaridar tace jirgin kirar 330 na daga cikin kadarorin wani attajirin dake harkar mai da ya mika shi ga bankin Jamus a matsayin jinginar karbar lamuni, daga bisani kuma aka sayar da shi.
Bayanai sun ce wani kamfanin sufurin jiragen Amurka da ake kira L&L dake Miami Florida ne ya jagoranci yarjejeniyar sayarwa Najeriya jirgin a kan sama da dala miliyan 100.
Jaridar Premium Times ta bayyana cinikin a matsayin garabasa saboda yadda farashin jirgin ayau kan iya kai wa dala miliyan 600 kamar yadda wani jami'in fadar shugaban kasa ya shaidawa jaridar.
Kasaitaccen jirgin na alfarma yanzu ya zama jirgin shugaban kasa da ake kira 'Nigeria Air Force One' mai lamba 5N-NGA.
Jami'in fadar shugaban kasar ya ce sabon jirgin ya ci kudinsa saboda kayan alatun dake ciki da kuma inagancinsa la'akari da girma da kuma kimar shugaban Najeriya a idon duniya.
Sai dai har yanzu rahotanni na nuna cewar Majalisar dattawa bata sanar da amincewa a sayo jirgin ba, duk da mahawarar da ta yi akan muhimmancin sauyawa shugaban kasar sabon jirgi, ya yin da babu wani bayani daga fadar shugaban dangane da wannan ciniki.
Wasu 'yan Najeriya sun fara bayyana bacin ransu dangane da cinikin a daidai lokacin da akasarin talakawan kasar ke fama da rashin abincin da za su ci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI