Najeriya ta fada cikin yaƙin basasa ne daga watan Yulin shekarar 1967 zuwa 15 ga watan Janairun shekarar 1970, bayan juyin mulkin sojin da ya hallaka akasarin shugabannin kasar na fararen hula.
Tsohon shugaban 'yan tawaye Kanal Chukwuemeka Ojukwu ya jagoranci tawayen da yunkurin kafa ƙasar Biafra, yayin da sojojin Najeriya a ƙarƙashin shugaban ƙasa na wancan lokacin Janar Yakubu Gowon suka ƙaddamar da yaƙi a kan su tare da samun galabar tabbatar da ƙasar a matsayin dunƙulalliya.
Daga bisani gwamnatin Najeriya ta ware wannan rana ta 15 ga watan Janairu domin tunawa da irin gudumawar da sojojinta suka bayar wajen dunƙulewarta da kuma tabbatar da tsaronta wanda ya kai ga rasa rayukan da dama daga cikin su.
A duk irin wannan rana ta 15 ga watan Janairu, akan gudanar da bukukuwa a matakan kasa da jihohi, inda shugabannin kan aje furanni domin tunawa da sojojin da suka sadaukar da rayukansu, tare da gudanar da faretin soji domin girmama su.
Baya ga tabbatar da ɗorewar Najeriya a matsayin ƙasa guda, sojojin Najeriya sun bada gudumawa a matakai daban daban na yaƙe-yaƙen ƙasashen duniya, ciki har da yaƙin duniya na 2 da yaƙin Congo da Liberia da Saliyo da Sudan da makamantansu.
Sai dai har ya zuwa wannan lokaci wasu daga cikin sojojin da suka bada gudumawar na korafi a kan rashin kula da su ko kuma iyalan wasu daga cikin su da suka sadaukar da rayukansu wajen daga tutar Najeriya.
A halin yanzu sojojin Najeriya na ci gaba da gudumawa wajen tinkarar yakin sunkuru tsakaninsu da 'yan ta'addan boko haram da ISWAP a yankin arewa maso gabashin kasar, yayin da wasu kuma ke fuskantar matsalar 'yan bindiga ɓarayin shanu da na ƙungiyar Lakurawa a yankin arewa maso yamma da kuma arewa ta tsakiya.
RFI Hausa ta tintibi tsohon kakakin sojin Najeriya, Janar Sani Usman Kukasheka wanda ya yi tsokaci akan muhimmancin wannan ranar da kuma yadda ake mayar da hankali wajen tuna irin gudumawar da dakarun sojin kasar suka bayar a matakai daban daban.
Janar Kukasheka ya ce irin wannan karramawar na daɗa basu ƙwarin gwuiwar cewar aikin da suka yi bai tafi a banza ba, domin mutane da kuma hukumomi na yabawa da shi.
Tsohon kakakin sojin ya ce baya ga su da suka tsira da rayukansu akwai wasu da dama da suka sadaukar da rayukansu da kuma wadanda suka jikkata a matakai daban daban a yunkurin su na ɗaga tutar Najeriya.
Janar Kukasheka ya ce hukumomi na kara ƙai mi wajen tallafawa iyalan irin waɗannan sojoji da suka rasa rayukansu ko kuma suka yi ritaya, duk da ya ke 'yan magana na cewa 'idan dambu ya yi yawa ba ya jin mai ba'.
Tsohon Daraktan yaɗa labaran ya ce abin alfahari ne a gare shi yadda hukumomin ƙasashen duniya ciki har da Majalisar ɗinkin duniya ke yabawa da irin gudumawar da sojojin Najeriya suke bayarwa a sasanta rikice-rikice daban-daban na ƙasashen duniya wanda shi da kansa ya taka rawa a cikin su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI