Rahotanni sun ce tuni tsoffin shugabannin biyu suka isa birnin Paris domin gurfana a gaban alkalin kotun sasanta rikicin kasuwanci sakamakon karar da kamfanin Sunrise Power ya shigar, inda yake bukatar Najeriya ta biya shi kusan dala biliyan 2 da rabi saboda soke kwangilar na dala biliyan 6.
Bayanai sun ce tsohon ministan wutar gwamnatin Obasanjo Olu Agunloye ya bada kwangilar ga kamfanin Sunrise ba tare da sanin shugaban kasa ko kuma amincewar majalisar zaratrawar lokacin ba.
Daga bisani gwamnatin da ta biyo baya ta soke kwangilar saboda rashin bin ka'ida wajen bayar da ita.
Jaridar The Cable da ake wallafawa a Najeriya ta ce tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ministan shari'ar Najeriya bayani dangane da abinda ya sa ni a kan harmcaciyar kwangilar da kuma nesanta kansa daga bai wa ministan shari'arsa Abubakar Malami damar shiga wata yarjejeniya ta daban domin bai wa kamfanin Sunrise dala miliyan 200 a matsayin diyya domin sasanta matsalar.
Kamfanin Sunrise ya shigar da kara a kotun Paris tun ranar 10 ga watan Oktobar shekarar 2017 inda yake bukatar a biya shi diyyar dala biliyan 2 da miliyan 354 akan kwangilar da kuma wasu karin dala miliyan 400 saboda abinda ya kira kin aiwatar da yarjejeniyar sasantawar da bangarorin biyu suka shiga a shekarar 2020.
Rahotanni sun ce tsoffin shugabannin Najeriyar Obasanjo da Buhari duk sun amince su bada shaida a kan shari'ar domin kare Najeriya daga zambar da ake neman mata.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jinjinawa tsoffin shugabannin saboda amincewa su kare martabar Najeriya a kan wannan badakala da wasu ke neman cin riba a ciki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI