Yaran da aka kame a zanga-zangar yunwa sun galabaita bayan tsarewar kwanaki 93

Yaran da aka kame a zanga-zangar yunwa sun galabaita bayan tsarewar kwanaki 93

Kwanaki 93 kenan ƙananan yaran waɗanda galibinsu suka fito daga arewacin Najeriya ke tsare a hannun mahukuntan ƙasar duk kuwa da tanadin dokar da ya nemi tsare mutum na sa'o'i 48 kaɗai gabanin yanke masa hukunci.

Hotunan yaran su 125 yayin bayyanarsu a gaban kotun sun nuna yadda matsananciyar yunwa ta galabaitar da su tare da fitar da su daga hayyacinsu, batun da ya haddasa cecekuce tsakanin al'ummomin sassan arewacin ƙasar.

Wasu daga cikin yaran da mahukuntan Najeriya suka tsare tsawon kwanaki 93. Wasu daga cikin yaran da mahukuntan Najeriya suka tsare tsawon kwanaki 93. © dailytrust

Rahotanni sun ce galibin yaran shekarunsu ya fara ne daga 15 zuwa ƙasa kuma tun a shari’ar da ta gabata cikin watan jiya kotu ta nemi 67 cikin 76 mafiya ƙarancin shekaru da ke cikinsu su biya Naira miliyan 10 kowannensu don samun beli baya ga samun wanda zai tsaya musu da ya kai mataki na 15 a aikin gwamnati, duk kuwa da kasancewarsu ƴaƴan marasa galihu da suka fito zanga-zangar ƙalubalantar halin yunwar da suke fama da ita.

A kalamansa bayan fitar bayanan halin da ƙananun yaran ke ciki da kuma kiraye-kirayen da ake masa na ganin ya shiga tsakani, babban mai shigar da ƙara Atoni Janar na Najeriyar Lateef Fagbemi ya ce yanzu ne ya ke da masaniyar cewa ƴan sanda sun kame tarin ƙananan yara kuma sun tsare su a gidan yari biyo bayan zanga-zangar ta EndBadGovernance a watan Agusta.

A cewar Fagbemi wasu daga cikin yaran ana tuhumar da tarin laifuka ciki har da cin amanar ƙasa, wanda ke nuna akwai buƙatar bincikar lamarin a ƙarƙashin ofishinsa gabanin cewa wani abu.

Tuni dai kotu ta yi umarnin ci gaba da tsare yaran har zuwa watan Janairun sabuwar shekara, batun da Fagbemi ke cewa ofishinsa ba shi da hurumin sauya matsayar shari’a, amma za a mika batun ofishinsa don fara bibiyarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)