Shugaban Asusun na UNICEF a jihar Borno Dr. Tushar Rane ya ce rashin abinci mai gina jiki na ƙara fadada a a yankin, yana mai cewa wannan ta sa UNICEF ta hada gwiwa da Ma’aikatar Ƴada Labarai don magance wannan matsala.
Yace a yanzu ƙididdiga ta nuna cewa yara sama da miliyan 2 da dubu 800 ne ke fama da wannan a jihohin, kuma wannan matsalar ta shafi har mata masu juna biyu, da ke fama da ƙarancin kiwon lafiya baya ga abincin.
Dr. Rane ya ce matuƙar ba a ɗauki matakin da ya kamata cikin gaggawa ba, wannan matsala za ta shafi ƙarin yara da mata sama da miliyan ɗaya da dubu 700 a bana kawai.
Ya ce a halin da ake ciki mata dubu 206,779 ne suke fama da ƙarancin abinci mai gina jiki, da kuma rashin samun hanyoyin kiwon lafiyar da ta dace da su.
Da yake jadadda ƙididdigar, wakilin na UNICEF ya ce cikin adadin yaran da ke fama da wannan matsala a jihohi, jihar Borno na da kaso 10 sai Yobe da ke da kaso 8 yayin da adamawa ke da kaso 4 cikin dari na adadin yara da ke fama da wannan matsala a Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI