'Yar Ado Bayero ta roki shugaba Tinubu da gwamna Abba da su saya musu gida a Lagos

'Yar Ado Bayero ta roki shugaba Tinubu da gwamna Abba da su saya musu gida a Lagos

Zainab Ado Bayero tace kuncin rayuwa ya sanya basu da matsugunin da za su zauna a Lagos, ganin cewar an tashe su a gidan da suke haya saboda kudinsu ya kare, kuma yanzu a otel suke zama saboda rashin kudin da za su mallaki gida na kan su tun bayan rasuwar mahaifinsu.

'Yar tsohon Sarkin wadda ta yi zargin cewar ba su samu komai ba daga gadon mahaifinsu, kuma rasuwarsa ta sanya su tozarta ta bayyana cewar gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya taimaka wajen biyan kudin hayar gidan da suke kafin a kore su, amma abinda suke bukata shi ne matsuguni na kansu a Lagos wanda akalla zai ci naira miliyan 150 da kuma kudin makarantar kaninta da kuma 'dan abin sana'ar da zata yi.

Zainab ta ce bayan korafin da ta yi, Gwamna Kabir na Kano ya tura mai magana da yawunsa Sanusi Bature wanda ya je ya biya kudaden hayar da ake bin su, amma kuma bayan haka iyalan na cikin matukar kuncin rayuwa saboda babu mai kula da su, ya yin da ta yi zargin cewar iyalan tsohon Sarkin sun yi watsi da su saboda babu mai taimaka musu.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar a jiya 23 ga watan Agusta kudin otel din su ya kare, kuma basu da wani matsugunin da za su zauna.

Zainab ta roki shugaban kasa Bola Tinubu da Gwamna Abba Kabir da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da kuma sauran 'yan Najeriya da su taimaka wajen saya musu gidan da za su zauna a Lagos.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)