'Yan sanda a Najeriya sun bankaɗo wata kwalejin koyar da damfara ta Internet

'Yan sanda a Najeriya sun bankaɗo wata kwalejin koyar da damfara ta Internet

Bayanan farko-farko na ‘yan sanda sun ce an gano kwalejin ne a ƙauyen Rantya da ke ƙaramar hukumar Jos ta kudu.

‘Yan sanda sun ce sun kama mutane 11 cikin su har da ɗalibai da kuma malaman kwalejin.

Ta cikin bayanin da kwamishinan ‘yan sandan jihar Emmanuel Adesina yayi, yace an kama mutanen ne a wani keɓaɓɓen gida da ake da yaƙinin cewa mahukuntan kwalejin ne suka kama hayarsa.

Da yake holen mutanen da aka kama, kwamishinan ‘yan sandan yace jama’ar yankin ne suka baiwa jami’an tsaro bayanin sirri kan kwalejin da kuma yadda take tafiyar da aikinta, nan take kuma jami’an tsaro suka baza komarsu.

An kama mutanen ne tare da wasu ƙarin ‘yan fashi, ‘yan bindiga da kuma masu garkuwa da mutanen da aka daɗe anan nema.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)