
Ministan ayyuka na Najeriyar Sanata David Umahi ya ce cikin hanyoyin har da babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano wanda ya zama wajibi masu binta su riƙa biyan kuɗin hanya ga gwamnati.
Umahi yace dukkanin hanyoyin da zarar aka kammalasu ɗari-bisa-ɗari ya zama wajibi gwamnati ta fara karɓar kuɗaɗen harajin hanyar na toll gate don yin amfani dasu wajen gyare-gyare ga hanyoyin ba tare da barinsu sun lalace ba.
Ministan lokacin daya kai ziyarar ganin yadda aikin hanyar ke gudana ya ce amma fa dokar fara karɓar harajin ba za ta fara aiki ba har sai an kammala shimfiɗa titunan an kuma fara amfani da su gadan-gadan.
Ministan ayyukan na Najeriya ya ce daga ranar 1 ga watan da muke ciki na Fabarairu, za a ɗauki tsawon watanni 14 gabanin kammala shimfiɗa titin na Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano, kuma da zarar an kammala shi jama’a za su fara biyan harajin hanyar.
Ƙasa da mako guda kenan bayan da gwamnatin Najeriya ta sanar da shirin fara karɓar harajin hanya a kan babbar hanyar Abuja zuwa Makurɗi wanda ya gamu da kakkausar suka daga al'ummar ƙasar musamman masu bin hanyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI