Bayanan dake fitowa daga birni na nuna cewar da ranar yau ake shirin masa jana'iza.
Obobo ya fara amfani da keken hawa ne wajen tafiya kasar Saudi Arabia ta hanyoyi masu hadari, tafiyar da ta sa shi ya yi suna da kuma samun karbuwa a wurin jama'a.
Rahotanni sun ce hukumomin Saudiya sun bukaci sayen keken da ya yi amfani da shi domin aje shi a matsayin tarihi amma marigayin yaki, inda ya dawo da shi Najeriya ya kuma mikawa gidan tarihin Lagos domin kula da shi.
Tuni labarin rasuwarsa ya karade kafofin sada zumunta inda mutane da dama ke ci gaba da sharhi a kan marigayin da kuma jajircewarsa wajen tafiyar kafa zuwa garuruwa ba tare da la'akari da haduran dake tattare da shi ba.
Alhaji Obobo tare da Editan RFI Hausa Bashir Ibrahim Idris © RFI HAUSADaga cikin wadanda suka yi sharhi da kuma tsokaci a kan rasuwar marigayin akwai fitaccen 'dan jarida Yakubu Musa, tsohon mai taimakawa shugaba Umaru Musa Yar'Adua a bangaren harkokin yada labarai, sai kuma Dr Idris Hamza Yana, malami a Jami'ar Jihar Jigawa.
Musa ya bayyana cewar ya dace a karrama irin bajintar da marigayin ya yi da kuma sanya shi cikin fitattun wadanda suka taka rawa a matakin duniya wajen cimma burin da ya saka a gaba a rayuwarsa ba tare da la'akari da masu sukarsa ba.
Daga cikin garuruwan da Obobo ya yi tattaki zuwa cikin su da kuma ganawa da Sarakunansu, akwai birnin Kano inda ya gana da Sarki Muhammadu Sanusi da Sokoto, inda ya gana da Sarkin Musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar da Minna, inda bai samu damar ganawa da tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida ba saboda rashin lafiyarsa.
Musa ya bayyana cewar abin takaici ne yadda wasu 'yan Najeriya suka ki ba shi wurin da ya dace da shi na gwarzo kamar yadda ake yiwa irinsu a kasashen yammacin duniya.
Dr Hamza Yana yace akwai darussa sosai da za'a kowa a rayuwar Obobo, ciki harda cimma burinsa na tuka keke zuwa Saudi Arabia domin sauke farali, sabanin yadda yanzu aka koma tafiya ta jirgin sama da kuma rashin gazawa wajen cimma manufarsa duk da yadda wasu ke masa shagube a kan manufofinsa.
Malamin jami'ar kuma tsohon 'dan jarida ya kuma tabo batun sanya muhimmanci a bangaren kula da lafiya a duk lokacin da mutane suka dauki tafarki irin na marigayi Obobo domin bincikar halin da jikin su ke ciki.
Yanzu haka an kaddamar da zaman makoki domin alhinin rasuwar wannan fitaccen jarumi Alhai Obobo da ake yiwa lakabi da 'Legend'.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI